Skip to content

Yadda ake special offal sauce

Bookmark (0)

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake special offal sauce cikin sauki. Wannan sauce na da saurin hadawa ga kuma dadi. Ba a bawa yaro mai kiwuya.

Abubuwan hadawa

 1. Dafaffen kayan ciki (ki yanka su kanana)
 2. Tarugu (ki jajjaga)
 3. Albasa (ki yanka)
 4. Karas (yanka shi kanana)
 5. Cucumber (fere bayan ki yanka shi kanana)
 6. Ganyen ugu (wanke ki yanka )
 7. Lawashi (ki yanka)
 8. Kayan kamshi
 9. Maggi

Yadda ake hadawa

 1. Daura tukunyanki akan wuta ki sa man gyadanki ko butter ki yanka albasarki ki soya sama sama, sai ki kawo kayan ciki ki sa a ciki ki juya ki soya sama sama shima.
 2. Dauko tarugu, albasa ki sa ki kawo gishiri kadan, maggi (iya dandano da zai miki) ki sa, kayan kamshi shima ki sa a ciki.
 3. Sai ki zuba ruwan zafi kadan ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya dauko shanyewa.
 4. Sai ki kawo ganyen ugu ki sa, cucumber, lawashi da karas ki zuba sannan ki juya ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin kadan. Sai ki barsu su turaru saannan ki sauke ki zuba a plate. A na iya cin wannan sauce da taliya, macaroni, farar shinkafa da dai sauransu. A ci dadi lafiya.

How many stars is worth this recipe?

As you found this recipe interesting...

Follow us on social media to see more!

Share this recipe on social media.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free recipes remaining!
×