Uwargida ga yadda ake plantain chips cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi uku ne kawai da steps uku.
Abubuwan hadawa
- Danyar plantain
- Gishiri kadan
- Mai
Yadda ake hadawa
- Ki samu danyar plantain ki yanka ta falan falan. Sai ki barbada gishiri kadan ki juya ko ina ya ji.
- Ki daura mai akan wuta in ya danyi zafi sai ki zuba ki soya, in ya yi sai ki tsane. A ci lafiya.
- Mai karatu wannan shine yadda ake plantain chips. Sai mun sake saduwa a girkinmu na gaba. Na gode, za ku iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake Zobo juice da makamantansu.