Skip to content

Yadda ake peppered soup na kaza

Share
yadda ake hada peppered soup na kaza
0
(0)
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Peppered soup na kaza ai duniya ce! Assalam alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya Kitchen. A yau zan koya mana yadda ake hada peppered soup na kaza.

Abubuwan hadawa

  1. Kazan Hausa
  2. Tarugu da tattasai
  3. Albasa
  4. Lawashi
  5. Curry
  6. Maggi da seasoning
  7. Tafarnuwa
  8. Tandoori Chicken spice

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki wanke kaza sosai sai ki zuba ta a cikin tukunya ki zuba ruwa ba masu yawa ba.
  2. Ki yanka albasa ki zuba da tafarnuwa ki rufe. Ki bari ya yi mintina 19 yana dahuwa.
  3. Sai ki bude ki zuba grated tattasai da tarugu, da seasoning, da lawashi da sauran kayan hadi.
  4. Ki rage albasa da za ki zuba karshe kadan. Idan ya dahu sai ki zuba sauran albasa ki bata minti daya ki sauke. Ba a so a cika ma peppered soup ruwa. Amfanin garlic da albasa yana cire duk wani kazni. A ci lafiya.
    Za a iya duba: Yadda ake hada rolled stuffed moi-moi da yadda ake liver sauce da sauransu.

How many stars will you give this recipe?

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page