Skip to content

Yadda ake hada rolled stuffed moi-moi

Share |
Yadda ake hada rolled stuffed moi-moi
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ga yadda ake rolled stuffed moi-moi mu koya ‘yanuwa. ku gwada wannan moi-moi mai kyau da kuma dadi. Kar ku bari a baku labari.

Abubuwan hadawa

 1. Wake
 2. Tarugu da tattasai
 3. Albasa
 4. Maggi da seasoning
 5. Garlic
 6. Manja
 7. Sausage
 8. Kwai
 9. Karas

Yadda ake hadawa

 1. Da farko za ki wanke wake ki surfa sai ki zuba tarugu da tattasai da albasa ki nika shi ya yi laushi sosai.
 2. Ki zuba wannan hadin a cikin bowl ki sa manja, seasoning, garlic powder, da curry, sannan za ki iya saka cray fish ma ki juya shi sosai komai ya hade.
 3. Ki saka mai kadan a pan ki sa sausage da karas ki yi stir frying na su sai ki sauke. Ki dafa kwai ki bare shi ki yanka slices. Shi ma ki aje a gefe.
 4. Za ki kunna oven 180° sai ki dauko parchment paper ki shinfida ta akan tray na baking ki zuba kullun ki saka a oven.
 5. Bayan mintina 10 in ya fara yi sai ki sauko da shi ki zuba fillings ko ina ki mayar ya gama gasuwa.
 6. Idan ya yi za ki ji kamshin ya hade ko ina ki sa toothpick ki duba, don kin tabbatar ya dahu. Ki sauke ki nade kaman nadin tabarma. Ki dan bari ya huce sai ki yanka. A ci lafiya.

Rate the recipe.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading