Skip to content

Yadda ake liver egg sauce

yadda ake liver egg sauce
3
(6)

Ku koyi yadda akeliver egg sauce cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi goma da kuma steps hudu

Abubuwan hadawa

  1. Kwai
  2. Dafaffafiyar hanta (yanka shi kanana)
  3. Tarugu (ki yanka)
  4. Tumatur (ki yanka)
  5. Koren tattasai (ki yanka)
  6. Maggi
  7. Kayan kamshi
  8. Gishiri kadan
  9. Man gyada
  10. Albasa (ki yanka)

Yadda ake hadawa

  1. Dauko kwano mai dan girma ki fasa kwanki a ciki ki buga shi sosai, sai ki ajiye a gefe.
  2. Daura tukunyanki a kan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama, sai ki kawo tarugu ki sa ki juya ki soya sama sama shima, kawo hantarki ki sa ki juya.
  3. Anan sai ki sa kayan kamshi, maggi da gishiri kadan iya dandano da zai mi ki ki juya nadan wani lokaci, sai ki kawo ruwan zafi dan daidai ki sa (ruwan kadan za ki sa) sai ki juya ki barshi nadan wani lokaci.
  4. Sai ki kawo tumatur ki sa ki juya sannan ki zuba kwanki ki sa a ciki ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin kadan, ki na juyawa (dan kar ya kama) ki na rufe tukunya yana turara, da zarar kinga ruwan ciki ya shanye sai ki kawo koren tattasai ki sa a ciki ki juya sai ki sauke. A zuba a gefen soyayyen Dankalin turawa ko doya da dai sauransu. A ci dadi lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×