Skip to content

Yadda ake pancake

Share |
Yadda ake pancake
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Uwargida ga yadda ake pancake cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi bakwai da kuma steps hudu.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi 1¼
  2. Madarar gari kofi ¼
  3. Kwai 3
  4. Ruwa ½ kofi
  5. Baking powder karamin cokali 1½ (tsbn)
  6. Flavor karamin cokali 1
  7. Suga kofi 1

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko filawanki ki dan tankade a cikin kwano mai dan zurfi, ki sa baking powder, da madarar gari, sai ki juya, sannan ki ajiye a gefe.
  2. Dauko wani kwano daban ki fasa kwanki a ciki sai ki zuba suga, sai ki ta juya shi sosai har sai suga ya dauko narkewa. Sai ki dauko hadin filawanki, ki dauko garin kwanki shima ki juye akan filawa sai ki sa ruwa da flavour ki juya har sai ya hade jikansa ya yi sumul.
  3. Sai ki ajiye shi na minti 15 a cikin fridge. Bayan minti 10- 15 sai ki dauko ki juya ki daura non stick pan na ki akan wuta (wutan ya zama kin rage shi sosai) idan ya yi zafi sai ki shafa mai kadan a cikin kaskon (kadan za ki shafa).
  4. Sai ki diba cokali 2 ko 3 na kullinki ki zuba a cikin kaskon ki rufe da murfi nadan wani lokaci har sai kinga ya fara koyi koyi (bubbles) a saman, sai ki juya dayan gefe shima ki gasa, idan ya yi sai ki sauke. Haka za ki yi har sai kin gama da kullinki.

Karin bayani

Ana iya zuba zuma ko jam ko nutella a kai idan za a ci. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×