Skip to content

Yadda ake offal sauce

Yadda ake offals sauce
5
(1)

Ga yadda ake offal sauce cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi goma ne da steps uku kacal.

Abubuwan hadawa

  1. Dafaffen kayan ciki (ki yanka kanana)
  2. Cucumber (ki yanka)
  3. Tarugu da tattasai (ki jajjaga)
  4. Carrots (ki gurza)
  5. Tumatur (ki yanka)
  6. Albasa (ki yanka)
  7. Man gyada
  8. Maggi
  9. Kayan kamshi
  10. Lawashi

Yadda ake hadawa

  1. Daura tukunyanki akan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama, sai ki dauko tarugu da tattasai ki sa ki soya sama sama.
  2. Dauko dafaffafen Kayan ciki nan ki sa a ciki ki juya sai ki sa ruwa kadan (ko ruwan silale) ki juya, dauko maggi da kayan kamshinki ki sa a ciki ki juya ki rufe tukunyanki na dan wani lokaci kadan har sai ruwan ya ragu.
  3. Daga karshe sai ki kawo carrot, cucumber, lawashi ki sa ki juya ki rufe nadan wani lokaci ya turaru sai ki sauke.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×