Skip to content

Yadda ake miyar wake

yadda ake miyar wake
5
(1)

Ku koyi yadda ake miyar wake. Wannan miyan waken tana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Wake
  2. Manja
  3. Attarugu
  4. Bushenshen kifi (banda)
  5. Albasa
  6. Maggi
  7. Kori
  8. Cittah       
  9. Tafarnuwa
  10. Gishiri

Yadda ake hadawa

  1. Da farko dai zaki wanke wakenki ya fita sosai
  2. Sai ki dora ruwan ki a wuta ya tafasa, sai ki zuba wakenki ya yi ta dahuwa har sai ya nuna ya yi lukwui
  3. Sai ki zuba jajjagaggen attarugu, da albasa, da manja, da kifinki, sai ki jira miyanki har sai ya tatafasa. Za ki ji yana kamshi
  4. Sai ki zuba maggi, da kori, da cittah, da tafarnuwa, da gishiri, sai ki barshi kamar minti sha biyar za ki ji gida ya dau kamshi
  5. Da zarar kin duba miyarki tayi shikenan sai ki sauke
  6. Zaki iya cin miyanki da tuwon shinkafa ko masara ko semonbita

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×