Skip to content

Yadda ake miyar vegetable soup

Share |
yadda ake vegetable soup
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku karanta yadda ake miyar vegetable soup mai annashuwa da kayatarwa.

Abubuwan hadawa

 1. Alaiyaho
 2. Ganyen ugu
 3. Tarugu da albasan (a jajjaga)
 4. Maggi (iya dandanonki)
 5. Gishiri kadan
 6. Curry
 7. Kifi soyayye
 8. Dafaffafen naman (ki yanka shi Kanana )
 9. Man gyada
 10. Daffafen kifi (za ki cire kayan sai ki farfasa shi)

Yadda ake hadawa

 1. Ki gyara kuma ki yanka alaiyahonki da ganyen ugu naki sai ki tafasa ruwan zafi . Idan ruwanki ya tafasa sai ki ki zuba akai nadan wani lokaci (bawai za ki bari ya jima bane kawai yadanyi laushi ne)
 2. Ki tsane alaiyaho da ganyen ugun a matsami sai ki matse ruwan jiki ya fita, sai ki ajiyeye a gefe.
 3. Ki sa tukunyanki akan wuta ki sa man gyada kadan ki yanka albasa ki soya sama sama
 4. Ki kawo tarugunki ki sa a ciki, sannan ki dauko yankakken namanki ki sa a ciki shima ki soya sama sama
 5. Sai ki kawo kayan kamshi, curry ki sa a ciki ki kawo maggi ki sa (ya danganta da irin dandanonki) sai gishiri kadan sai ki juya
 6. Ki dauko soyayyen kifinki ki sa a ciki ki juya (idan zaki sa kifin da kika farfasa a anan ya kamata ki sa)
 7. Sai ki dan sa ruwa kadan ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin (ruwan kadan za kisa )
 8. Daga karshe kuma ki dauko ganyenki ki zuba a ciki, sai ki juya a hankali ki rufe tukunyanki yadan turara nadan wani lokaci sai ki sauke.

Rate the recipe.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading