Skip to content

Yadda ake miyar kubewa mai ugu

Share |
Yadda ake miyar kubewa mai ugu
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake miyar kubewa mai ugu. Wannan miyan kubewa ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!

Abubuwan hadawa

  1. Kubewa danya
  2. Ganyen ugu
  3. Dafaffafen kifi
  4. Nama da cray fish
  5. Manja
  6. Maggi
  7. Albasa
  8. Tarugu
  9. Kayan kamshi
  10. Kanwa
  11. Gishiri kadan
  12. Danyen kubewa daban kamar guda 5

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko kubewa ki wanke ki yanka ta sai ki sa a blender ki sa masa ruwa dan daidai da kanwa ko markada sai ki ajiye a gefe, dauko tarugu ki jajjaga ajiye a gefe sai dauko ganyen ki gyara ki wanke sai ki yanka, sannan ki dauko kubewa (wanda ki ka ware guda 5) ki yanka ta kanana kanana sai ki ajiye su a gefe.
  2. Daura tukunyanki akan wuta ki sa naman ki a ciki ki yanka albasa ki sa kayan kamshi, gishiri kadan ki rufe ya tafasa sosai nadan wani lokaci , har sai ya nuna. Sai ki dauko daddawa ki sa, maggi (iya dandanon da zai mi ki) ki sa, sai ki kara ruwa kadan ki rufe nadan wani lokaci sai ki dauko dafaffafen kifinki ki sa a ciki ya kara tafasa sosai.
  3. Sannan ki dauko kubewa ki sa (wanda ki ka nika) ki sa a ciki ki juya sai ki kawo tarugu ki sa da manja ki sa ki na juyawa a hankali har sai ya nuna.
  4. Daga karshe sai ki dauko ganyen ugu (wanda ki ka yanka da kubewa) sai ki zuba ki juya a hankali har sai ganyen ya yi laushi. A ci dadi lafiya. Ana iya cinsa da tuwo, tuwon shinkafa, amala, eba da dai sauransu.

Karin bayani

Idan ki na so miyanki ta yi yauki sosai kar ki rufe tukunya ki kawai sai dai ki na juyawa a hankali har sai ya nuna.

Rate the recipe.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading