Skip to content

Yadda ake mini cake loaf

mini cake loaf 1
0
(0)

Cake kala-kala ne, kuma hanyoyin sarrafa shi suna da yawa wadda cikin su akwai mini cake loaf. A yau na kawo maku yadda ake mini cake loaf, wani cake mai sauki, mai taushi, sannan mai dadi da kyau ko a ido.

Mini Cake Loaves wani nau’in ƙaramin cake ne mai kama da burodi (loaf), wanda yake da sauƙin ci da kuma ɗauka. Ana yin su ne da kayan haɗi kamar fulawa, sukari, ƙwai, madara, da bota, tare da ƙarin flavors ko ɗanɗano iri-iri kamar vanilla, chocolate, strawberry, ko lemun tsami. Saboda ƙaramin girmansu, suna da matuƙar dacewa da bukukuwa, tarurruka, liyafa, da kuma matsayin kyauta.

Abubuwan Bukata:

1- 1 cup margarine

2- 3/4 cup sugar

3- 4 eggs

4- 3 tablespoons evaporated milk

5- 1 teaspoon flavor of choice

6- 2 cups flour

7- 1/4 teaspoon salt

8- 1/2 teaspoon baking powder

9- 2 tablespoons crushed oreos

10- 2 tablespoons crushed lotus biscuits

Yadda ake yi:

Domin samun mini cake loaf mai dadi da kyau, a bi wadannan matakan masu sauki.

1- Za ki fara zuba sugar da margarine a cikin bowl sai ki mixing dinsu da electric handmixer ko kuma heavy duty whisk har sai sun zama light and fluffy.

mini cake loaf 2

2- Sai ki dinga zuba kwan da kika fasa kadan-kadan kina mixing.

mini cake loaf 3

3- Next, sai ki zuba madara da flavor dinki ki cigaba da mixing dinsu.

mini cake loaf 4

4- Ki zuba dry ingredients dinki (flour, salt, and baking powder) sannan kiyi mixing har sai komai ya hade.

mini cake loaf 5

5- Sai ki samu mini cake loaf pans dinki, ki zuba batter din a ciki gently, sannan ki barbada crushed oreo biscuit dinki a saman su (zaki iya amfani da kowani irin biscuit).

mini cake loaf 6

6- Daga nan sai ki dauka ki kai a pre heated oven ki gasa a medium heat da wutar kasa kadai sai ta kusa gasuwa ki kunna ta sama.

mini cake loaf 7

7- Shikenan mini loaf cake dinki ya hadu. Za ki iya cin sa da black tea, papaya mocktail ko duk lemun da ake so asha dashi.

8- Idan kina so ma, zaki iya kara sarrafa mini cake loaves dinki ta kara sinadirai daban-daban kamar su mini chocolate loaf, mini lemon loaves da sauran su.

Aci dadi lafiya!

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×