Skip to content

Yadda ake meat stuffed potato

Meat stuffed potato
0
(0)

Dankali na ɗaya daga cikin abincin da ake amfani da shi sosai a duniya saboda sauƙin sarrafa shi da kuma irin muhimmancin da yake da shi. Ana iya dafa shi, soyawa, gasa shi ko kuma haɗa shi da sauran kayan abinci domin samar da nau’o’in abinci masu armashi. Daya daga cikin shahararrun hanyoyin sarrafa dankali shi ne yin Meat Stuffed Potato, wato dankali da aka cika da nama, dafaffen kwai, da kayan haɗi masu ɗanɗano.

Meat stuffed potato abinci ne matuƙar daɗi kuma ana iya cin sa a matsayin abin karin kumallo, abin ci na rana ko kuma abin da za a gabatar wa baƙi a wajen taron biki ko shakatawa. Haɗuwar dadin dankali da ɗanɗanon naman da aka soya tare da kayan ƙamshi yana samar da wani irin ɗanɗano na musamman wanda mutane da yawa ke so.

Meat stuffed potato yana da amfani sosai saboda yana ƙunshe da sinadarai masu gina jiki. Dankali yana ba jiki kuzari saboda yana ɗauke da carbohydrates, yayin da nama ke samar da protein wanda yake taimakawa wajen gina jiki da ƙarfafa tsoka. Idan aka ƙara kayan lambu da kayan ƙamshi, abincin yana ƙara armashi da amfani ga lafiya.

Wannan girki ba shi da wahala idan aka bi matakai yadda ya kamata. Ana iya yin sa ta hanyoyi daban-daban; wasu suna amfani da dafaffen dankali, wasu kuma suna amfani da soyayyen dankali. Haka kuma ana iya amfani da naman sa, naman kaza, har ma da naman kifi ko dai duk abinda mutum yake so.

Abubuwan hadawa

  • Dankali 10
  • Kwai 2
  • Albasa 2
  • Attarugu 2
  • Nama
  • Maggi
  • Gishiri
  • Mai
  • Curry/Thyme

Yadda ake hadawa

Abi waɗannan matakai yadda ya kamata don samun meat stuffed potato mai dadi da armashi.

  1. A fere dankali, a wanke sannan a dafa da dan gishiri kadan amma kada dafa shi ya dahu gaba daya dan kada ya tumurmushe wajen suya.
  2. A tafasa nama idan ya dahu a daka ko a nika ta inji irin kiran VTCL Excella.
  3. Sai a soya shi sama sama tare da albasa da Attarugu.
  4. A dafa kwai daya, sai a yanka kanana kanana ko ayi mashing din shi da potato masher ko manual food masher.
  5. A sa Maggi gishiri curry da thyme da kayan kamshi.
  6. A danyi yanka ta gefen da yafi tsawo a jikin dankalin yanda zai bada dama a samu a kwakwule cikin dankalin.
  7. Idan kuma za’a iya cire dan murfin saman dankalin sai a yi hakan.
  8. Sannan a kwakwule cikin dankalin a zuba hadin naman a ciki( amma kar a kwakule cikin dankalin gaba daya).
  9. Bayan nan sai a maida murfin a rufe ko adan matse shi ko a dan yi masa rufi da dankalin da aka kwakwule da kada naman da aka zuba aciki ya zube acikin man.
  10. Next sai a tsoma a ruwan kwai sannan a sa a mai a soya har sai yayi kalar gwal wato golden color.
  11. Za’a iya cin sa da kunun gyada, kunun couscous ko da shayi mai zafi.

akasrin bayani: Za’a iya yin meat stuffed potatoes ta wani samfarin wato a gasa shi acikin oven din gashi. Haka kuma za’a iya yin sa da dankalin hausa wato sweet potato ko red potatoes.

Aci dadi lafiya!

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×