Skip to content

Yadda ake meat pie

Share |
yadda ake meat pie
Add to Lists (0)

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake meat pie mai ban sha’awa ga dadi ga kuma kyau. Wannan gangariyar meat pie idan uwargida ta gwada zata bamu labari!

Abubuwan hadawa

  1. Filawa
  2. Butter
  3. Salt
  4. Baking powder
  5. Dafaffen nama
  6. Dankali turawa (ki dafa shi)
  7. karas (ki gurza shi)
  8. Maggi
  9. Kayan kamshi
  10. Mai kadan
  11. Albasa
  12. Tarugu
  13. Kabeji

Yadda ake hadawa

Dought

  1. Ki samu bowl ki sa filawa sai ki sa butter ko man gyada sai ki samu egg ki sa ki kwaba sosai.
  2. Sai ki sa ruwan (ruwan dai-dai yadda zai karasa kwaba miki filawar ki) sai ki kwaba shi sosai. Ba a so ya yi ruwa-ruwa, ya yi dai-dai yadda za a iya murza shi a sa filling. Ki ajiye a gefe.

Filling

  1. Ki samu nama ki tafasa ki yanka ko ki daka sai ki daura pan na ki a kan wuta ki kawo naman ki, ki jajjaga attarugu da albasa, mai kadan sai ki dauko dankali (dama kin yanka su kanana) da su karas shima ki hada ki sa.
  2. Ki kawo kayan kamshi, maggi gishiri kadan daga ki sa.
  3. Daga karshi ki kawo kabeji ki sa sai ki juya ki dan soya su sama-sama sai ki ajiye a gefe.
  4. Ki dauko kwabin filawarki ki murza da abun murza filawa ya yi fadi (ki yanka shi da dan fadi ya baki 4 corners) sai ki zuba fillings
  5. dinki ki rufe ki samu folk ki danna bakin din (edge) sai ki soya a mai. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×