Skip to content

Yadda ake kosai mai laushi

Share |
yadda ake kosai
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake kosai mai laushi ga dadi ga kuma kyau. Wannan kosai ana bukatan kayan hadi takwas ne domin hada ta.

Abubuwan hadawa

  1. Wake
  2. Albasa
  3. Tattasai
  4. Attarugu
  5. Gishiri
  6. Maggie
  7. Kwai
  8. Ruwa

Yadda ake hadawa

  1. Ki wanke wake ki gyara ki sa albasa, attarugu da tattasai ba dayawa ba sai a kai miki nika. Ki ce kar su cika miki ruwa. Bayan an kawo nikar, ki sa gishiri kadan da maggi (in ki ka sa maggi da yawa kullun ki zai yi baki. Kar maggin su wuce biyu in kullun na ki daidai misali ne).
  2. Sai ki sa ruwa kadan in kullun ya na da kauri.
  3. Ki fasa kwai ki buga kullun ki sosai za ki ga kullin tana canza color into a lighter one. Samun nika mai kyau da kuma bugu shine zai sa kosai ya yi kyau. Kwai kuma na kara masa laushi kuma in kina soyawa zakiga yana tashi mai kyau.
  4. Idan man ki ya yi zafi sai ki soya. Saboda idan man bai yi zafi ba kullun zai warwashe a ciki. A ci lafia.

Rate the recipe.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake kosai mai laushi”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading