Skip to content

Yadda ake hadin dambun nama

Share |
yadda ake hada dambun nama
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

A yau za mu ko yi yadda ake hadin dambun nama.

Abubuwan hadawa

  1. Nama mara kitse kilo
  2. Attarugu
  3. Maggi 
  4. Albasa
  5. Gishiri
  6. Tafarnuwa
  7. Cittah
  8. Mangyada
  9. Kori

Yadda ake hadawa

  1. Da farko zaki wanke namanki ki sa albasa da maggi ki dora a wuta ki tafasa ya nuna sosai.
  2. Idan yayi sai ki sauke ki kawo turminki mai kyau ki daka namanki ya daku sai ki kwashe.
  3. Sai ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa da cittah ki zuba akan dakekken namanki kisa, sannan ki sa maggi da kori ki juya sosai komai ya hadu.
  4. Idan yayi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mangyada ki zuba namanki ki yi ta juyawa har sai yayi yanda kike bukata.
  5. Idan yayi sai ki sauke ki juye a wani abu mai kyau.

Na gode.

Photo Credit: Funke Koleosho

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×