Skip to content

Yadda ake hada miyar alayyaho (veg soup)

Share |
yadda ake hada miyar alayyahu
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

A yau kuma zan koya mana yadda ake hada veg soup ne wato miyar alayyaho.

Abubuwan hadawa

  1. Tattasai da tarugu
  2. Manja
  3. Nama
  4. Albasa
  5. Seasoning da spices
  6. Allayyaho
  7. Lawashi

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki tafasa nama ki sa albasa a cikin tafashen da maggi. Idan ya yi sai ki juye ki zuba manja ki sa nama, sai ki zuba wannan chopped tattasai da tarugun da albasa mai yawa ki juya sai ki dan rufe ya soyu kaman mintina 3.
  2. Bayan kamar minti ukun, sai ki bude ki saka yan ruwa kamar kofi 1/4, ba da yawa ake so ba. Ki sa seasoning da spices, ki yanka albasa da lawashi da allayaho ki wanke ki zuba, ki rufe idan ya dahu a ci.

Za a iya dubaYadda ake dambun shinkafa mai gyada da yadda ake hada healthy spinach mix da sauransu.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×