Skip to content

Yadda ake hada local jollof rice

Share
Yadda ake hada local jollof rice
0
(0)
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

A yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafadukan shinkafa ke nan da Hausa.

Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa
  2. Tattasai da tarugu
  3. Daddawa
  4. Albasa
  5. Seasoning
  6. Manja
  7. Tafarnuwa
  8. Busashshen kifi
  9. Danyen nama

Yadda ake hadawa

  1. Farko zaki dora tukunya ki zuba manja a ciki ki yanka albasa. Sai ki wanke nama ki zuba a ciki.
  2. A dai dai wannan lokacin uwargida ta gyara kayan miya (tattasai tarugu da albasa) sai ki zuba a cikin wannan naman ki juya, za ki ga yana dan soyuwa sama sama, sai ki tsayar da ruwan dahuwar shinkafarki.
  3. Ki zuba tafarnuwa, daddawa da maggi da sauran seasoning a cikin ruwan sannan ki rufe.
  4. Idan ya tafasa sai ki wanke shinkafa ki zuba ki rufe. Ki yanka albasa manyan slices sai ki gyara kifi busashe ki hade su.
  5. Idan shinkafarki ta fara tsotse ruwa sai ki zuba ki rufe su dahu tare. Idan ya dahu a sauke.

Za a iya duba: Yadda ake platain sauce da yadda ake hada tuna muffins da sauransu.

Photo Credit: Immaculate

How many stars will you give this recipe?

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page