Skip to content

Yadda ake hada juice na abarba da kankana

Share |
Yadda ake hada juice na abarba da kankana
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Mu koyi yadda ake hada juice na abarba da kankana cikin sauki. Wannan juice ne mai dadi, da karin lafiya da kuma saukin kayan hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Kankana
  2. Abarba
  3. Sugar
  4. Flavour

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki cire yayan kankana sai ki sa a blender ki gyara abarba itama ki sa sai ki sa ruwa ki yi blending na su baki daya.
  2. Idan ya yi sai ki tace ki sa sugar da flavour da kankara.

Banbancin tsakanin juice da smoothie da kuma milkshake

  1. Idan ki ka yi blending wannan kayan marmari (fruits) kawai har sai ya niku lumus ki sa kankara, to wannan SMOOTHIE ne.
  2. Idan kuma, bayan nikan, ki ka tace shi, to wannan JUICE ne.
  3. Idan ki ka nika ki ka sa ruwa da madara wanann MILKSHAKE ne ke nan. Ina fata an gane wannan bayani. A sha lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×