Skip to content

Yadda ake grilled chicken

Grilled chicken 1
0
(0)

Akwai hanyoyi da dama na sarrafa kaza ko grilled chicken. Grilled chicken wani hanyar sarrafa kaza ne mai dadi da ake yi ta hanyar gasa naman kaza a kan wuta ko tanda tare da kayan yaji da kayan kamshi. Wannan gashin yana da matukar armashi saboda dandanon kayan yaji da laushin naman da ake samu bayan an gasa shi sosai. Mutane da yawa suna son grilled chicken saboda yana da saukin hadawa kuma ana iya ci da abinci iri-iri kamar su shinkafa, dankali, ko salad.
A yau na kawo hanya na sarrafa grilled chicken cikin sauki domin sannan mai dadi, matukar kuka gwada za ku ji dadinsa.

Abubuwan bukata:

1- 1 big chicken

2- 1 teaspoon honey

3- 1/2 teaspoon parsley flakes

4- 1/2 teaspoon black pepper

5- 1 cup pepper mix

6- 1/2 onion

7- 1 teaspoon ginger and garlic paste

8- 2 tablespoons maggi powder

9- 1/2 teaspoon salt

10- 1 tablespoon oil

11- 1 sachet chicken seasoning

13- 1 tablespoon dakakken yaji

Yadda ake yi:

1- ki wanke kaza tas, ki zuba a pot, ki saka albasa, dandano, ginger and garlic paste, sai ruwa kadan, ki bari ta dahu amma ba tubus ba. Sai ki samu kyakkyawan bowl dinki, ki zuba pepper mix wanda sai da kika tafasa shi da kayan kamshi sannan kika markada, sai ki saka zuma, parsley, da chicken seasoning

2- ki saka mai, black pepper, dakakken yaji, sannan ki motsa da kyau komai ya hade.

3- Then ki dauko tafasasshiyar kazarki ki tsoma a wannan hadin da kika yi, ki tabbatar komai ya kama ta sannan ki saka a fridge na awa daya zuwa awa biyu. Daga nan sai ki jera a kan baking tray ki gasa na minti arba’in zuwa awa daya.

4-Shikenan grilled chicken dinki ya hadu. Ki fitar dasu aga oven dinki ki jera a kan rack ki bar su su dan huce na minti kadan. Za’a iya cin sa da lemun cucumber, soyayyen dankali ko shinkafa ko duk wani abunda ake so a hada da shi. Wannan grilled chicken din bata da kishiya.

Aci lafiya!

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×