Skip to content

Yadda ake funkaso

Share |
Yadda ake funkaso
Add to Lists (0)

No account yet? Register

 A wannan fannin a yau za mu koyi yadda ake funkaso, funkaso wani abinci ne da jama’a da dama ke sha’awa musamma ma a Arewacin Najeriaya.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa
  2. Yeast
  3. Gishiri kadan
  4. Man gyada na suya

Yadda ake hadawa

  1. Ki tankade filawarki ki sa gishiri kadan sai ki ajiye a gefe.
  2. Dauko yeast na ki, ki sa masa ruwan dumi (ruwan dumi ba mai zafi ba) da suga (karamin cokali) ki juya, sai ki rufe ki ajiye a gefe kamar na tsawon minti 3, idan ya na da kyau za ki ga ya yi kumfa ya kumbura (amfanin yin hakan don ki san yeast din mai kyau ne).
  3. Sai ki juye yeast din cikin filawanki kidan kara ruwa ki kwaba shi kamar kwabin fanke sai ki rufe ki kai rana ya tashi Kamar minti 20-30 idan ya taso sai ki kara buga shi sosai ki ajiye a gefe.
  4. Ki dauko kasko ki daura kan wuta, ki zuba man gyada idan ya yi zafi, sai ki na diban kwabin funkaso nan kadan kadan ki na fadada shi da hannunki ki na sawa a mai ki na soyawa har sai ya soyu, sai ki tsane a matsani. Ana iya ci funkaso da miyan stew, miyan taushe, Ko miyar ganye. A ci dadi lafiya.

Wannan shine yadda ake funkaso. Na gode, sai Allah Ya sake hada mu a girki na gaba .

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×