Skip to content

Yadda ake faten shinkafa

Share |
yadda ake faten shinkafa
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ga yadda ake faten shinkafa na zamani da surkin gargajiya.

Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa
  2. Alaiyaho da yakuwa (ki gyara ki yanka su, ki wanke da gishiri)
  3. Albasa mai lawashi (ki yanka)
  4. Maggi (ya danganta da irin dandano ki)
  5. Tarugu (ki jajjaga)
  6. Albasa (ki yanka)
  7. Manja mai kyau (ki soya)
  8. Gyadar miya zaki dakata (optional)
  9. Dafaffafen nama ko kifi banda (ya danganta da irin wanda kike so)

Yanda ake hadawa

  1. Da farko ki sa tukunyanki akan wuta ki sa ruwa yanda zai isheki ki dafa shinkafar ki. Har ya danyi ruwa ruwa (tunda fate akace) Saiki wanke shinkafarki ki zuba a ciki ki barshi yayita tafasa har sai kinji ta fara laushi.
  2. Sai ki dauko tarugu ki sa ki kawo maggi, nama ko kifi, curry, kayan kamshi da gishiri ki sa daidai dandano da zai miki.
  3. Ki dauko manja ki sa, sai ki kawo ganyen lawashi ki zuba a ciki, daga karshe kuma ki dauko gyada ki zuba sai ki juya a hankali. Sannan ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin (amma ki na juyashi a hankali nadan wani lokaci) har sai komai ya nuna.

Rate the recipe.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading