Ga wani dabaran yadda ake egg in a hole bread mai dadi da kuma sauki. Cikin kalilan lokaci, uwargida zaki hada komai.
Abubuwan hadawa
- Brodi mai yanka
- Kwai
- Mai kadan
Yadda ake hadawa
- Da farko za ki samu burodinki mai yanka sai ki nemi cutter ( round ) ki danna cutter a sakiyan borodin zai yanka sai ki cire na sakiyan ki ajiyeta a gefe.
- Ki sami frying pan ki sa mai kadan sai ki daura burodin na ki a ciki.
- ki fasa kwai a tsakiyan round inda ki ka cire burodin, ki dan gasa in ya yi sai ki juya dayan gefen shima ya yi.
Karin bayani
Na sakiyan da ki ka cire shima za ki iya gasawa ki ci.
Kada ki cika wuta ya yin gasa burodin