Croissant wani irin burodi ne mai dadi da laushi wanda ya shahara sosai a ƙasashen turai da yawa, musamman a Faransa tunda daganan ya samo asali. Wani snack dinsu ne wanda suka mayar da shi na al’adarsu, kamar dai a ce gurasa ga Bakano.
Ana yin sa ne da fulawa, butter, yisti, sukari, da madara ko ruwa. Ana yawan cin croissant ne da chuku wato cheese, chocolate, madara ko da shayi ko coffee, kuma yawanci ana cin sa ne da safe a matsayin karin kumallo.
Ingredients
1- 2 cups flour
2- 1 egg
3- 1 tablespoon yeast
4- 1/2 teaspoon salt
5- 2 tablespoons sugar
6- 1/4 cup vegetable oil
7- 125g butter
8- 1/2 cup liquid milk
Yadda ake yi:
Domin hada croissant mai hadadden dadi, abi wadannan matakai masu sauki ba tare da bata lokaci ba.
1- Ga jerin abubuwan da muke da bukata

2- ki zuba madararki a cikin bowl, sai ki zuba yeast, egg, oil, flour, salt.

3- Ki hada soft dough. Bayan nan sai ki rufe shi ki bari ya tashi na akalla minti talatin

4- Ga shi nan bayan ya tashi

5- Sai ki raba shi gida takwas. Sannan ki yi moulding din kowanne

6- sannan ki yi flattening dinsa da rolling pin. Ki dora a kan tray ki shafe shi da butter. Ki sake flattening wani ki dora a kan wancan shi ma ki shafe da butter. Haka za ki yi har sai kin yi duka guda takwas din. Ana so duka su zama equal sizes.

7- Daga nan sai ki rufe shi ki sa a fridge ya yi minti arba’in zuwa awa daya haka.

8- Ga shi nan bayan kimanin awa daya.

9- Sai ki barbade shi da flour ki dora a kan working surface ki yi flattening dinsa da fadi sosai

10- Sai ki yanka shi kamar haka da pizza cutter.

11- Sannan ki nannada ko wani part da kika yi cutting ki bar su for around 30minutes haka ko har sai yayi doubling in size.

12- Bayan kinga sun tashi yanda ya kamata sai ki shafa masu kwai kiyi coating saman saboda ya yi golden brown din da ake so bayan gashi.

13- Sai ki sa a oven ki gasa na 30 minutes.
14- Bayan sun gasu sai ki chiro ki bari su dan sha iska. Zaki iya cin croissant dinki da shayi ko duk wani lemu da kike sha’awan ci dashi.
Karin bayani: Zaki iya filling croissant dinki ma idan kina so, wato filled croissants kamar yadda ake filled doughnuts. Ana iya hada cream cheese croissants, chocolate croissants, almond croissants da sauran su.
Aci dadi lafiya !





