Skip to content

Yadda ake couscous jollof

Share |
Yadda ake couscous jollof
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake couscous jollof cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi sha uku da kuma steps hudu.

Abubuwan hadawa

  1. Couscous
  2. Tarugu
  3. Karas
  4. Maggi
  5. Kayan kamshi
  6. Peas
  7. Koren wake
  8. Cucumber
  9. Tsokar kifi
  10. Masarar gwangwani
  11. Gishiri
  12. Albasa
  13. Daddawa

Yadda ake hadawa

  1. Daura tukunya a kan wuta ki sa mai sai ki kawo tarugunki ki sa ki kawo albasa ki sa ki soya sama sama sannan ki kawo kayan kamshi, da daddawa ki sa da maggi, da gishiri (iya da zai miki) sai ki soya sama sama.
  2. Sannan sai ki kawo tsokar kifin ki ki sa ki juya sannan ki kawo tafashashshen ruwa ki sa (ruwan iya wanda zai dafa miki couscous na ki) sai ki juya ki rufe tukunya ki nadan wani lokaci.
  3. Da zarar kinga ya fara watsartsara sai ki kawo couscous na ki ki zuba a ciki ki rufe tukunya ki, sannan ki rage wuta sosai nadan wani lokaci.
  4. Daga karshe, sai ki kawo su koren wake, karas (kin dan basu tsoro da ruwan zafi, sannan a ruwan zafi ki sa baking powder), sai ki kawo masarar gwangwani (itama ki tsane ruwan da ke jikin ta kafin kisa) sai ki juya a hankali ki barsu sudan turara a ciki sai ki sauke. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

2 thoughts on “Yadda ake couscous jollof”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading