Skip to content

Yadda ake coconut milk balls

Share |
yadda ake coconut milk balls
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

A girkin namu na yau zamu koyar da yadda ake coconut milk balls ne.

Abubuwan hadawa

  1. Kwakwa (irin na leda ko kanti)
  2. Madara ta gari
  3. Condensed milk
  4. Sugar
  5. Chocolate
  6. Mai kadan

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko kwanonki babba, ki zuba madararki a ciki ki kawo kwakwa ki zuba sai ki sa condensed milk a ciki ki kawo mai kadan ki sa.
  2. Sai ki kwaba shi ya kwabu sosai sai ki shafa mai a tafin hannu ki, ki na diba kadan kadan ki na fadada shi ki na sa chocolate a tsakiyan kina mulmula shi har sai ya baki ball. Haka za ki yi har sai kin gama da sauran kwabinki.
  3. daga karshe, sai ki barbada sugar a kai ki sa a fridge ya yi kamar minti 20, sai ki cire. Shi ke nan coconut milk balls na ki ya kammala.  A ci dadi lafiya.

Wannan shine yadda ake coconut milk balls mai karatu. Na gode, sai Allah Ya hada mu a girki na gaba. Amma kafi nan, mai karatu na iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake cake mai kala uku da Yadda ake farfesun dankali da makamantansu.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×