Skip to content

Yadda ake coconut cupcakes

Share |
Yadda ake coconut cupcakes
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake coconut cupcakes cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi bakwai da kuma steps shida.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi hudu (4 cups)
  2. Kwai 15 (ya danganta da irin girmansu)
  3. Butter 2 (simas leda 2)
  4. Baking powder karamin cokali hudu (4tsp)
  5. Filebo karamin cokali uku
  6. kwakwa (na yi amfani da na kwali dan Kanti)
  7. Suga kofi biyu (ko kofi biyu da rabi)

Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki tankade filawarki tare da baking powder, sai ki ajiye a gefe.
  2. Ki sami mixer machine na ki ki sa butterki a cikin wannan kwanon mixer (ko ki sami wani kwano daban idan da hand mixer za ki yi) ki yi ta motsa shi na dan wani lokaci.
  3. Ki kawo suga ki sa a ciki ki yi ta motsa shi har sai suga ki ya narke a ciki (ba kijin gudajin sugar a cikin butter) Sai ki dauko kwai ki fasa ki yi ta motsa shi (Kwan ana so ana sa shine daya bayan daya kuma ana motsa shi bayan kowani sa kwai da aka yi) har ki gama da kwanki.
  4. Sai ki dauko vanilla filebo ki sa ki motsa. Ki dauko filawanki da ki ka tankade tare da baking powder (za ki iya raba filawar gida shida) ki rinka zubawa a hankali a cikin wannan hadin butter har ki gama da flour ki na motsa shi.
  5. Bayan kin gama zuba filawarki sai ki dauko bushashshen kwakwa ki zuba ciki ki motsa. Sai ki dauko abin gashin (nakan sa takakardar gashi a cikin abin gashin kafin na zuba kwalli cake nawa).
  6. Ki zuba hadin kwalli ki a cikin kowani takardar gashi (ba a so a cika shi don kar ya zube a lokacin gashi, ki sa su rabi rabi ko yadanfi rabi da kadan don ya yi gashi mai kyau) Sai ki sa a cikin magasa (prehated oven) ki gasa, har sai ya gasu (ko idan kinsa tsinke ya fito ba tare da komai a jikin sa ba) sai ki cire ki bari yasha iska. A ci dadi lafiya

Rate the recipe.

Average: 2.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading