Skip to content

Yadda ake Chinese spaghetti

Share |
yadda ake chinese spaghetti
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake Chinese spaghetti ga dadi ga kuma kyau. Wannan hadin Chinese spaghetti din na da saukin gaske wajen yi.

Abubuwan hadawa

 1. Kwai
 2. Spaghetti
 3. Karas (ki gyara ki yanka dogo dogo)
 4. Koren wake (ki yanka)
 5. Ganyen curry
 6. Tarugu (ki jajjaga)
 7. Kayan kamshi
 8. Maggi
 9. Mai
 10. Albasa (ki yanka)
 11. Gishiri kadan

Yadda ake hadawa

 1. Daura tukunya babba akan wuta ki sa ruwa idan ya tafasa ki sa taliyar ki a ciki (ba sai kin karya ta ba) idan ya yi rabin dahuwa ki zuba mata ruwa ki tsane a matsani. Ajiye a gefe.
 2. Dauko kwanki ki fasa ki sa maggi, da gishiri kadan ki kawo albasa ki sa. Ki buga shi sosai. Ajiye agefe.
 3. Daura pan na ki akan wuta ki sa mai kadan ki zuba tarugu kadan sai ki sa ruwa kadan idan ya tafasa sai ki kawo kwanki ki zuba a ciki ki rufe nadan wani lokaci sai ki bude kina juya shi a hankali har sai ya fara dunkulewa (Scrambled), idan ya yi yanda ki ke bukata sai ki sauke a gefe.
 4. Sake daura tukunya akan wuta ki sa mai kadan ki kawo albasa ki soya sama sama sai ki kawo tarugu ki sa, kayan kamshi, da maggi, da gishiri iya dandanon da zai mi ki ki sa, ruwa kadan (iya daidai wanda zai karasa miki dafa taliyar ki) ki sa ki juya ki barshi nadan wani lokacin har sai ya fara tafasa.
 5. Sai ki kawo taliyar ki zuba a ciki ki juya ki kawo kwanki (wanda ki ka yi a baya) ki zuba sai ki juya ki sake zuba albasa da ganyen curry. Sai ki rufe nadan wani lokacin har sai ruwan jikin ya shanye sai ki kawo karas, da koren wake ki sa ki juya ki bar shi su dan turara a ciki. Sannan, sai ki sauke. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading