Skip to content

Yadda ake boiled plantain and egg sauce

yadda ake boile plantain and egg sauce
3.7
(3)

Ku koyi yadda ake boiled plantain and egg sauce cikin sauki. Wannan recipe na bukatan kayan hadi bakwai ne da steps guda biyar.

Abubuwan hadawa

  1. Plantain (agada)
  2. Kwai
  3. Tumatur
  4. Tarugu
  5. Man gyada
  6. Maggi
  7. Kayan kamshi

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko agada ki bare bawon ki yanka su ajiye a gefe. ki daura tukunya wuta ki sa ruwa idan ya tafasa sai ki kawo yankakken agada ki sa ki dafa ta kamar minti 5 haka.
  2. Sai ki sauke ki tsane shi a colender (matsani) ajiye a gefe.
  3. Daura wata tukunyanki akan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama. Sai ki kawo tarugu, tumatur da albasa ki zuba a ciki ki juya ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin kadan.
  4. Bude ki juya ki kawo kayan kamshi da gishiri kadan ki sa ki juya ki kawo maggi iya dandano da zai miki ki juya.
  5. Dauko wani kwano daban ki fasa kwanki a ciki sai ki juye a cikin hadin da ke wutan nan, ki barshi nadan wani lokaci sai ki juya a hankali har sai kwanki ya nuna miyar ki ta yi. Anan sai ki sauke ki zuba a plate ki kawo dafaffafiyar agadanki ki sa a gefe. A ci dadi lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×