Skip to content

Yadda ake banana milkshake

Yadda ake banana milkshake
2
(1)

Ku koyi yadda ake banana milkshake. Wannan milkshake ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!

Abubuwan hadawa

  1. Ayaba guda hudu
  2. Madarar gari cokaki hudu
  3. Ice cream scoop daya (In ba ki da ice cream sai ki sa madarar gari da yawa.)
  4. Kankara
  5. Suga yadda ake bukata

Yadda ake hadawa

  1. Ki samo blender ki sa kankara (crushed ice), ayaba, madarar gari, scoop na ice cream, suga in ki na bukata.
  2. Sai ki rufe blender ki yi blending har sai ya yi (till smooth) sai ki samu kofi ki zuba a sha. Shikenan milkshake ya hadu. Na gode sai mun hadu a girkinmu na gaba 

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×