Ku koyi yadda ake banana and coconut ice cream cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi bakwai ne da steps uku.
Abubuwan hadawa
- Ayaba
- Madarar kwakwa
- Madara
- Sugar
- Flavour
- kwakwa (ki gurza)
- Chocolate
Yadda ake hadawa
- Ki dauko ayaban ki bare ki yanka ta kanana ki sa a blender ki kawo madarar kwakwa, da madara (ta ruwa) ki sa ki zuba sugar iya yanda ki ke son zakin ya kasance.
- Sai ki markada ya markadu sosai sannan ki juye a roba ki sa a freezer ya yi kankara. Sai a sami cokali mai zurfi ki na diba ki na sawa a kofi, sannanki sa wani karamin kwano.
- Daga karshe ki yaryada chocolate a kai da gurjajjiyar kwakwa shima a kai. A sha dadi lafiya.
Dan Allah meye madarar kwa-kwa
Madarar kwakwa shine coconut milk. Ana sayarwa a kasuwa ko kuma za ki iya yi a gida. Yadda za ki yi a gida shine, ki samu kwakwarki ki cire bayan ki bar wannan farin kawai. Sai ki markada a blender, ki sa ruwa ki tace idan ya markadu, wannan ruwan shine madarar kwakwa.