Skip to content

Yadda ake alalen manja

Share |
Yadda ake alalen manja
Add to Lists (0)

No account yet? Register

Mu koyi yadda ake alalen manja cikin sauki, abubuwan hadawa guda goma ta hanyar bin matakai guda biyar kawai.

Abubuwan hadawa

 1. Wake
 2. Albasa
 3. Tattasai
 4. Attarugu
 5. Crayfish
 6. Manja
 7. Maggi star
 8. Gishiri
 9. Citta da tafarnuwa
 10. Ledan alale

Yadda ake hadawa 

 1. A wanke wake a cire bayansa tsaf.
 2. A yayyanka albasa a ciki, a sa tattasai da tarugu, a sa citta da tafarnuwa da crayfish, a kai aniko (wurin nikan ace nikan alale za’ayi)
 3. In an kawo nikan sai asa maggi da manja a hade ko ina yaji da kyau, sai a kukulla a leda.
 4. Asa a tukunya sannan asa ruwa a daura kan wuta har alalen ya dahu. Yadda za ki gane alale ya dahu shine za ki ga alalen ya bar jikin leda, wannan ya nuna cewa alale ya dahu.
 5. In ya dahu sai ki sauke. Ki daura wani manjan ki soya in ki ka zuba alalen a plate sai ki yayyafa soyayyen manjannan, ana hadawa da yajin borkono. Wayyo gargajiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×