Mu koyi yadda ake alalen manja cikin sauki, abubuwan hadawa guda goma ta hanyar bin matakai guda biyar kawai.
Abubuwan hadawa
- Wake
- Albasa
- Tattasai
- Attarugu
- Crayfish
- Manja
- Maggi star
- Gishiri
- Citta da tafarnuwa
- Ledan alale
Yadda ake hadawa
- A wanke wake a cire bayansa tsaf.
- A yayyanka albasa a ciki, a sa tattasai da tarugu, a sa citta da tafarnuwa da crayfish, a kai aniko (wurin nikan ace nikan alale za’ayi)
- In an kawo nikan sai asa maggi da manja a hade ko ina yaji da kyau, sai a kukulla a leda.
- Asa a tukunya sannan asa ruwa a daura kan wuta har alalen ya dahu. Yadda za ki gane alale ya dahu shine za ki ga alalen ya bar jikin leda, wannan ya nuna cewa alale ya dahu.
- In ya dahu sai ki sauke. Ki daura wani manjan ki soya in ki ka zuba alalen a plate sai ki yayyafa soyayyen manjannan, ana hadawa da yajin borkono. Wayyo gargajiya.