Skip to content

Yadda ake wainar semovita

Share |
Yadda ake hada wainar semovita
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Yau in sha Allah za mu koyi yadda ake wainar semovita anan shafin mu na Bakandamiya Kitchen.

Abubuwan hadawa

  1. Garin semobita
  2. Yis (yeast)
  3. Sukari
  4. Gishiri
  5. Albasa
  6. Man gyada
  7. Ruwan dumi

Yadda ake hadawa

  1. Dafarko zaki zuba garin semobitanki acikin kwano mai fadi
  2. Sai ki zuba yeast da sikari da gishiri daidai misali kamar dai yanda zaki zuba idan dai zaki yi wainar shinkafa
  3. Sai ki kawo ruwan duminki ki zuba ki na mai juyawa da muciya a hankali har sai kwa6in ya yi daidai da kullin wainar (ruwan dumin yana taimakawa kullin wajen tashi da wuri amma idan akwai rana zaki iya kwabawa da ruwan sanyi). Sai ki yi ta juyawa har na tsawon minti 15.
  4. Idan yayi zaki ga ya yi mulmul yana kamshi, sai ki rufe ki barshi a rana har sai ya tashi
  5. Idan ya tashi sai ki yanka albasa a cikin kullin, sai kuma ki dora tanda ko kasko (frying pan)
  6. Zaki ga tayi washar da ita kamar wainar shinkafa
    Ana cinta da miyar taushe ka romon naman kan rago ko kulikuli

A ci dadi lafiya. za ku iya duba yadda ake masa

Photo Credit: Ayyush Hadejia

Rate the recipe.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading