Na sani da yawan mutane ba su son spaghetti, musamman maza. Sai dai dayake akwai hanyoyi da yawa na sarrafa ta, babu mamaki idan kuka gwada wannan procedure din ku so ta.
Abubuwan bukata:
1- 1/2 sachet spaghetti
2- 2 bell peppers ( 1 red and 1 green).
3- 2 carrots
4- 8 green beans
5- 2 tablespoons maggi and onga powder
6- 1 teaspoon curry powder
7- 1/2 cup vegetable oil
8- quarter onion
9- 1 tablespoon light soy sauce
10- 1/2 teaspoon ginger and garlic paste
11- 1/2 sachet Mr chef mixed spices
12- 1 cup stock
Yadda ake yi:
1- ki zuba mai a cikin kyakkyawar tukunyarki irin ta Bakandamiya shopping. Sai ki sa albasa da ginger and garlic paste ki soya kadan sai kamshi ya fara tashi. Then ki sa carrots and green beans ki soya sama sama. Ki kawo light soy sauce ki zuba. Then ki sa toasted kayan miyan da kika markada su.

2- Sai ki zuba seasoning, curry, da mixed spices ki soya.

3- Then ki zuba per boiled spaghetti wadda kika sa gishiri wurin tafasa shi. Ki motsa da kyau komai ya hade. Sai Ki saka ruwan tafashen nama idan akwai. Idan babu kuma ki saka normal ruwa . Ki sa bell peppers

4- Sai ki motsa da kyau sannan ki rufe ki bari ya dahu na akalla minti goma sha biyar a low heat.

5- Daga nan sai ki sauke a yi serving da zafinta.

6- Na dora peri peri lamb a sama.
