Akwai hanyoyi da dama na sarrafa nama. Tun daga kan su farfesu, soyayye, miya, da sauransu. A yau na zo maku da yadda ake yin pepper meat hadadde na naman rago. Yana da saukin yi sannan yana da dadi.
Abubuwan bukata
1- 1kg lamb
2- 1 sachet tomato paste
3- 2 tablespoons maggi powder and 1 cube onga
4- 1 teaspoon salt
5- 2 tablespoons mixed spices
6- 1 ladle pepper mix
7- 1 teaspoon soy sauce
8- 1 teaspoon oyester sauce
9- 1 tablespoon sugar (optional)
10- 1 teaspoon curry powder
11- 1/4 cup oil
Yadda ake yi:
1- Ki wanke naman rago tas, sai ki dora a tukunya ki zuba albasa da spices (na yi amfani da paprika, rosemary, ginger and garlic powder). Sai ki zuba seasoning, ki zuba ruwa makimanci yadda ba zai yi yawa ba dan kadan ake so ya rage.

3- Ki rufe tukunyar ki bari ya dahu tubus akalla awa daya zuwa da rabi.

4- Sai ki tsame naman nan ki saka a cikin air fryer ki air frying na minti sha biyar idan ba ki da ita ki soya a cikin mai. Ko kuma ki duba shafin Bakandamiya Shopping ki sayi ingantacciyar Air fryer dinki ki huta da barnar mai.

5- Ki kwashe ragowar ruwan naman daga cikin tukunya. Ki zuba mai, albasa, tomato paste, curry, and spices ki soya har sai kin ji kamshi yana tashi. Alamun ya soyu ke nan

6- Sai ki zuba maggi, pepper mix (tattasai, tarugu da albasa). Ki zuba sugar amma ba dole ba ne sai dai yana kara masa dandano mai dadi. Ki bari su soyu sannan ki kawo wannan naman ki juye a ciki.

7- sai ki zuba ragowar ruwan naman nan, ki zuba soy sauce da oyester sauce ki motsa. Sannan ki rufe ki bari su hade jikinsu na minti bakwai zuwa goma a wuta low.

8- Daga nan sai ki sauke ki yi serving a kyakkyawan plate irin na Bakandamiya Shopping.
