Duk kuka ji an ambaci native, to wani abu ne ake nufi wanda ya shafi gargajiya. Taliyar gargajiya ce wadda na zamanantar. Ku biyo ni domin ganin yadda ake yi.
Abubuwan bukata:
1- 1 cup cooked beans
2- 1/2 sachet per boiled spaghetti
3- 1 handful alayyahu
4- 1/2 cup palm oil
5- 2 daddawa
6- 1/2 bunch garlic
7- 2 tablespoons maggi powder
8- 1 onion
9- 6 pieces cow tail
10- 2 cups leftover stew
Yadda ake yi:
1- ki zuba manja a cikin pot sai ki zuba jajjagen garlic da daddawa. Idan kika dan soya shi sai ki sa albasa da dafaffen cow tail

2- Sai ki kawo leftover stew ko kuma jajjagen kayan miya ki zuba ki soya.

3- Sai i zuba dafaffen wake da dafaffiyar taliya. Ki zuba dandano yanda zai ji.

4- ki juya da kyau sannan ki zuba ruwa kadan

5- sai ki zuba alayyahu, bayan minti biyar zuwa bakwai ta nuna sai ki sauke

6- ki yi serving a kyakkyawan plate
