Abin da ya sa na kira wannan cake din da local cake shi ne, asalin cake dai da muka sani tun na yarinta, wanda babu wani kanshi na flavor a cikinsa, amma sai matukar dadi. Sannan ingredients kadan ne amma yana da auki.
Abubuwan bukata:
1- 3 cups flour
2- 1 cup sugar
3- 1 sachet butter
4- 4 eggs
5- 1 tablespoon baking powder
6- 1/2 cup room temperature water
Yadda ake yi:
1- ki zuba butter a cikin bowl, sai ki zuba sugar ki mixing har sai ya zama light and creamy. Then ki kawo kwai shi ma ki zuba, ki sake mixing.

2- sai ki zuba baking powder da flour ki mixing da kyau. Za ki ga kwabin ya dan yi karfi. Daga nan dai ki zuba ruwa ki tsinka shi.

3- Ga yanda zai zama nan.

4- Sai ki greasing local gwangwanayenki na cake. Shi irin wannan ba a yi da liners na cupcake. Ainahin dandanonsa na gargajiyan ya fi fitowa idan a cikin gwangwani ne.

5- Daga nan sai ki dauka ki saka a oven wanda kika riga kika yi pre heating dinsa. Za ki gasa ne da wutar kasa kadai. Bayan ya gasu sai ki kunna wutar sama saboda saman ya yi golden brown ya fi kyau da dadi

6- Ga shi nan bayan ya gasu.

7- Bayan ya huce sai na yi packaging dinsa. Idan kika saka a leda bai gama hucewa ba yana sanya shi saurin lalacewa
