Skip to content

Lemun abarba da kwakwa

lemun abarba da kwakwa
5
(1)

Mu koyi yadda ake lemun abarba da kwakwa. Wannan juice yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Abarba  (madambaciya 1)
  2. Kwakwa  (babbah 1)
  3. Madara ta ruwa (1)
  4. Sukari kadan  (idan kina bukata)
  5. Abin kamshi (flavour)mai kamshin abarba da kwakwa

Yadda ake hadawa

  1. Da farko Uwargida  za ki wanke abarbanki kuma ki yanka kanana sannan ki zuba a blenda ki markada
  2. Idan ya markadu sai ki tace ki ajiye a gefe
  3. Ki fasa kwakwarki itama ki yanka kanana ki markada blenda
  4. Idan ya yi sai ki tace akan ruwan abarbar
  5. Sai ki zuba madara da suga (idan da  bukatar suga din) da abin kamshi
  6. Sai ki juya sosai sai kuma ki zuba kankara ko ki sa a furinji tayi sanyi dan tana bukatar sanyi

Photo credit: beautifuleatsandthings

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×