Ba koyaushe ba ne za ki dinga sarrafa nama ta hanyar da kika saba. A wasu lokutan yana da kyau ki sabunta. Dalilin haka ne ya sa na kawo maku yadda ake sarrafa lamb peri-peri.
Abubuwan bukata:
1- 1kg lamb meat (naman rago)
2- 1/2 cup oil
3- 1 tablespoon soy sauce
4- 2 tablespoons maggi da onga powder
5- 1 teaspoon curry
6- 1 large onion
7- 2 tomatoes
8- 1/2 green bell pepper
9- 2 tattasai
10- 4 attarugu
11- 1/2 tablespoon ginger and garlic paste
12- 1 tablespoon mixed spices
13- 2 maggi cubes
14- 2 tablespoons oil (extra)
15- 1 tablespoon parsley flakes
16- 1 tablespoon dakakken yaji
17- 1/2 sachet Mr Chef mixed spices
18- 1/2 lemon
Yadda ake yi:
1- Ki zuba kayan miya a cikin kyakkyawan pan irin na Bakandamiya shopping. Sai ki zuba mai, curry, ginger and garlic paste.

2- Idan kin yi toasting dinsu sama-sama sai ki kwashe ki saka a blender ki markada amma ba a zuba ruwa. Zallan man da yake jikinsu zai wadatar ki markada a kyakkyawar blender. Idan ba ki da ita ki leka Bakandamiya Shopping akwai masu kyau da nagarta.

3- a cikin wannan pan din za ki zuba nama, ki saka mixed spices sai seasonin cubes yanda zai ji.

4- Ki dan tsorata naman kadan na akalla minti goma sannan ki sauke ki zuba waccan sauce din da kika hada, ki motsa da kyau yadda zai kama shi. Then ki saka shi a fridge na minti talatin zuwa awa daya.

5- ki zuba mai a kyakkyawan kwano, sai ki sa yaji, busasshen parsley, mixed spices, soy sayce sannan ki matsa rabin lemon tsami.

6- Ki ciro naman daga cikin fridge sai ki juye a kan baking tray, ki shafe shi da wannan hadin da kika yi sannan ki saka a oven ki gasa da wutar sama da kasa na minti arba’in zuwa awa daya.

7- Ga shi nan bayan ya nuna.
