Kamar yadda kuka sani ana yin chicken mandi, wato mandi wadda ake yi da kaza. To haka ma ana yin ta naman rago. Tana da saukin yi sosai, sannan tana da dadi. Ku biyo ni ku ga yadda nake yin tawa.
Abubuwan bukata:
1- 3 cups basmati rice
2- 1 tablespoon mandi spice mix
3- 2 large onions
4- 1 and 1/2 cups oil
5- 1 kg lamb (wanda babu kashi ko jijiya)
6- 3 tablespoons seasoning powder
7- 5 cups water (or as required. Gwargwadon karfin naman)
8- extra 3 tablespoons of oil, 2 tablespoons pepper powder, 1/2 sachet tomato paste, 1/2 sachet inga powder.
For making the sauce:
1- 1 onion
2- 5 attarugu
3- 1/2 sachet tomato paste
4- 2 maggi cubes
5- 1 teaspoon curry powder
6- 2 tablespoons oil
Yadda ake yi:
1- Ki soya albasa har sai ta zama caramelized.

2- Bayan kin tsame albasar za ki bar kadan. Sai ki sa naman rago wanda ba a yanka shi ba. Ki zuba dandano da gishiri, sai mandi mix dinki.

3- ki zuba ruwa 4 cups. Then ki rufe ki bar shi ya dahu har sai ruwan ya tsotse a kan naman.

4- ki zuba mai da yaji a cikin bowl, sai ki sa ketchup ko tomato paste. Then onga powder (red saboda kalarsa ta kama kazar). Amma rabi za ki sa.

5- Idan ruwan naman ya tsotse ya rage kadan sai ki tsame shi, ki kara ruwa makimanci, then ki wanke basmati ki zuba a ciki.

6- Sai ki shafa wannan marinade din da kika hada. Ki tabbata ko’ina ya kai. Daga nan ki dora a gawayi ko oven ki gasa na minti sha biyar kina yi kina juyawa.

7- idan ruwan shinkafar ya tsotse kuma kin tabbatar ta dahu, sai ki zuba ragowar ongan nan daban daban, sannan ki kawo albasar da kika soya a farko ki juye sama. Ki dora foil paper da gawayi mai wuta, ki zuba mai da cloves guda biyu. Then ki rufe tukunyar na minti uku zuwa biyar.

8- Ita kuma sauce din, ki zuba mai da albasa, sai jajjagen tarugu. Then tomato paste ki soya sama sama. Ki zuba curry da seasoning ki bari ta soyu sannan ki sauke.

9- A yi serving a kyakkyawan plate irin na Bakandamiya shopping
