Skip to content

Hadin dankalin turawa na musamman

Hadin dankalin turawa na musamman
4.2
(9)

Ku koyi yadda ake hadin dankalin turawa na musamman. Wannan hadin dankali yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Dankali (Irish)
  2. Kwai 5
  3. Attarugu 4
  4. Albasa 2
  5. Maggi 4
  6. Gishiri
  7. Kori
  8. Tafarnuwa
  9. Koren tattasai 1
  10. Mangyada

Yanda ake hadawa

  1. Da farko zaki fere dankalinki kiyanka ki zuba gishiri kadan sai ki rufe ki dora a wuta ki tafasa.
  2. Idan yayi sai ki sauke ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa da cittah ki ajiye agefe.
  3. Sannan sai ki kawo tukunya mai fadi kamar kasko sai ki zuba mangyada ki dora a wuta kisa dankalinki, sannan ki zuba kayan da kika jajjaga.
  4. Sai ki juya a hankali, ki fasa kwainki, ki zuba maggi da kori sai ki juya har yayi. Idan yayi sai ki sauke ki juye.

Na gode. 

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×