Akwai hanyoyi da dama na sarrafa hanta. Wasu su yi sauce dinta, wasu tsire, wasu a saka a abinci. A yau na kawo maku yadda ake gashin hanta a cikin oven. Mai dadi, sannan mai sauki.
Abubuwan bukata:
1- 1/2 kg liver
2- 2 bell peppers (red and green)
3- 1 tablespoon maggi powder
4- 1/2 teaspoon salt
5- 2 tablespoons vegetable oil
6- 1 large onion
7- 1/2 teaspoon chili flakes
8- 1 tablespoons mixed spices
Yadda ake yi:
1- ki wanke liver sai ki yanka ta sirara. Ki zuba a cikin baking dish dinki. Sai ki zuba bell peppers da seasoning and spices

2- ki zuba mai da albasa

3- Ki zuba chili flakes amma idan kina son ya yi yaji kadan

4- Ki saka hannunki ki murtsuka komai ya shiga ciki da kyau

5- sai ki rufe da foil paper ki sa cikin oven a wutar sama da kasa ki gasa na minti arba’in zuwa awa daya.

6- Daga nan sai ki ciro shi daga cikin oven din a yi serving

7- Gashi nan na zuba sai ci.

Ku duba shafin Bakandamiya Shopping akwai baking dish da spoons da nau’ukan kayan kitchen masu kyau.