Kin taba jin alalen wake da doya? Idan baki taba ba, yau gashi mun kawo miki uwargida. Nemi wuri zauna ga step by step na yadda za ki yi.
Abubuwan hadawa
- Wake
- Doya
- Attarugu
- Albasa
- Maggi
- Kori (Curry)
- Tafarnuwa
- Kwai
- Gishiri
Yadda ake hadawa
- Da farko zaki wanke wakenki ya fita tas
- Sai ki fere doyarki ki yanka kanana sai ki zuba akan wakenki
- Sannan ki sa attarugu da albasa da tafarnuwa sai a kai miki markade
- Idan markadenki ya dawo sai ki zuba ruwan dumi da maggi, da gishiri, dakori, da manja, kuma dama (juya) daidan kaurin alalan
- Dama kin dafa kwanki ya na gefe. Sai ki rika daura kullunki a a laida ki na jefa kwan a ciki
- Idan kin gama daurawa, sai ki zuba a tukunya ki zuba ruwa ki dora a wuta ya samu kamar minti 45
- Da zaran ya dahu za ki ji gida ya dau kamshi. A ci dadi lafiya.
Ina son koya girke girke masu dadi na zamani