2 colours milk candy tuwon madara ne mai kyau da tsari. Wani version ne na sarrafa tuwon madara wadda take da kala biyu. Ana yi masa haka ne dan kara kayatarwa da kuma jan hankali, wanda yara da manya ke so. Bashi da wahalar yi ko kadan kuma yana da dadi sosai.
Za,a iya yin sa da flavors kala-kala da launauka iri-iri harda ma designs kala-kala kai har ma wanda bashi da design ana iya yi su duka. Yana da sauki da dadin yin kyauta da shi musamman ga kananan yara ko amatsayin abin jefawa a jakar souvenir wajen taron bukukuwa ko taron nishadi.
Haka zalika yana da sauki da kawo kasuwa ga masu son yin business din alawa ko masu son fara kasuwanci ma da shi.
Abubuwan bukata:
1- 1/3 cup water
2- 1/3 cup sugar
3- 1/2 teaspoon flavor
4- 2 cups milk
5- drop of pink color
6- 1 teaspoon strawberry flavor
Yadda ake yi:
1- ki zuba sugar da ruwa a pan ki bari su dahu har sai sugar ya gama narkewa duka a low heat. Sai ki zuba flavor ki motsa ya dan fara danko sannan ki kashe wuta. Ki zuba madara ki tuka.

2- Sai ki raba shi gida biyu; ki zuba food colour da strawberry flavor a ko wani kashi. Ki motsa da kyau har sai ya hade jikinsa sosai.

3- Sai ki dauko cutter dinki ta tuwon madara, ki dibi portion mai pink kala kadan ki zuba a ciki. Sai ki danna shi da kyau. Sannan sai ki dora cutter din a kan wancan white portion din da kika yi flattening. Sai ki ciro shi. Zaki iya amfani da maamoul silicon molds ko luxiv cake mold dan fitar da designs masu kyau.

4- Za ki gan design din ya fito kamar haka.

5- ki bar shi ya sha iska da kyau yanda babu danko ko baya kama hannu.

6- Sannan sai kiyi packaging din su duk yanda kike so kiyi. Zaki iya sa su acikin sweet

7- Shikenan kin kammala tuwon madara mai kala 2 dinki acikin sauki da kwanciyan hankali.
Aci dadi lafiya!





