Skip to content

Yadda za ki hada scones

Share |
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ina masoya kayan flour, ku zo ku koyi yadda ake scones cikin matakai masu sauki da bayanai masu gamsarwa.

Abubuwan hadawa

 1. Fulawa 3
 2. 1 cup icing sugar
 3. 125g butter (asaka ya yi sanyi)
 4. kwai 1
 5. 1 cup yoghurt
 6. Vanilla flavour
 7. Baking powder

Yadda ake hadawa

 1. Farko za ki zuba fulawa a cikin bowl, Ki tankade icing sugar ki saka, sai ki saka baking powder a ciki ki juya.
 2. Ki yi amfani da abun goga kubewa wato (grater) ki goga butter dinki a ciki. Sai ki juya su sosai har ya hade.
 3. Ki fasa kwai a ciki, ki dinga zuba yoghurt ki na hadawa har ki samu soft dough.
 4. Ki kara buga dough din sosai sai ki dora akan rolling board, ki yi rolling ki fitar da shapes ki samu bowl ki kada kwai daga sai ki saka brush ki yi egg wash na saman ko wane.
 5. Sai a gasa tsawon mintina 15, idan ya yi a cire a barbada icing sugar a kai. A ci lafiya

Kuna iya duba Yadda ake hada pineapple crush da sauransu.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading