Skip to content

Yadda za ki adana veggies na ki fresh

Share |
Yadda za ki adana veggies na ki fresh
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Uwargida ki duba yadda za ki adana veggies na ki fresh tsawon lokaci. Idan kun bi wannan hanyar to kunyi bankwana da lalacewar veggies ke nan.

Ire-iren veggies da za a adana

  1. Koren wake
  2. Karas
  3. Masarar gwangwani
  4. Peas na gwangwani
  5. Lawashi

Yadda za a adana su

  1. Ki gyara koren waken ki, ki yanka shi irin yankan da ki ke so ajiye a jefe. Ki sa ruwa akan wuta idan ya yi zafi sai ki sa baking powder ko ruwan kanwa a ciki ki kashe wuta sai ki kawo koren wake ki sa a ciki ki barshi nadan wani lokaci kadan .
  2. Sai ki tace ki sake wanke shi da ruwa mai kyau ki sa a matsani ki tsane sa ki tabbatar ba ruwa a jikinsa. Ajiye a gefe.
  3. Dauko peas, da masarar gwangwani ki pape bakinsa ki zuba su a roba sai ki sheka masa shima ki tsane a matsani. Ki tabbatar ba ruwa a jikinsu. Ajiye a gefe.
  4. Dauko karas ki goge dattin bayansa ki yanka shi irin yanka da ki ke so ki wanke ki tsane sa a matsani. Ki tabbatar ba ruwa a jikin sa. Ajiye a gefe.
  5. Lawashi shima ki wanke ki yanka ki tsane a matsani.
  6. Daga karshe sai ki dauko duka veggies na ki ki hadasu gu daya sai ki sa a freezer ya yi kankara. Duke lokacin da ki ke da bukata sai ki fito da shi yadan sha iska kafin ki yi amfanin ki da shi.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×