Skip to content

Yadda ake vegetable egg sauce

Share |
yadda ake vegetable egg sauce

Ku koyi yadda ake vegetable egg sauce ga dadi ga kuma kyau. Wannan egg sauce da saukin gaske wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Kayan lambu (karas da kabeji da koren wake da tattasai)
  2. Albasa
  3. Maggi
  4. Mai
  5. Kwai
  6. Tattasai da tarugu

Yadda ake hadawa

  1. Ki daura mai akan wuta, ki kawo albasa da yankakkun kayan lambu ki zuba, ki kawo maggi da jajjagen tarugu da tattasai suma ki zuba sai ki dan sa ruwa kadan ki motsa ki rufe na minti biyu.
  2. Idan ya yi ki bude ki fasa kwai akai sai ki gauraya da ludayi ki rufe na wasu mintuna biyun, sai a kwashe. 

Aci dadi lafiya, don dai gaskiya abin ba a cewa komi ni dai da doya naci. Mai karatu na iya karanta: Sauce din icefish da Yadda ake cabbage sauce da makamantansu.

Add to Lists (0)

No account yet? Register

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page