Ga yadda ake valentine cut-out cookie, mu koya ‘yanuwa. Wannan cookies ba za a so a baiwa yaro mai kiwuya ba. Ku gwada ku bani labari…
Abubuwan hadawa
- Butter kofi 1 (250grm)
- Simas kofi 1
- Sugar
- Kwai 4
- Milk kofi 1
- Baking powder cokali 1 (tspn)
- Flour kofi 4
- Vanilla cokali 1 (tspn) ko kuma duk irin flavour da ki ke bukata
Yadda ake hadawa
- A cikin mixer, ki hada butter da sugar, ki yi mixing na su har sai sun hade sun zama kamar ruwa, sannan babu alamun sugar a ciki.
- Daga nan, sai ki rika sa kwan ki a cikin hadin, daya bayan daya ki na juyawa, sannan sai ki sa milk, da baking powder sannan ki sa vannila duk a cikin hadinki.
- Annan sai ki sa filawar ki a cikin hadin ki kwaba su gaba daya.
- Daga nan sai ki cire dough din ki, ki sa akan kitchen table ko wani wuri mai tsabta. Sai ki kara hada shi da kyau a wannan wajen sai ya dahu sosai ya yi dai dai.
- Ki sa a fridge na awa daya ko kuma in cikin dare ne ki sa shi ya kwana a fridge din.
- Ki fitar, ki murza, sannan ki yi cutting na shi yadda ki ki so da abin cutting na cookies.
- Ki gasa shi a oven na ki a temperature 120° na kamar minti 20 har sai ya yi (ki madara).
- Sai ki yi decorating na shi duk yadda ki ke bukata. Na kan yi amfani ne da Royal icing don yin decoration na cookies, musamman wajen buki ko suna.