Ina Amaren mu na zamani? Ku shirya tsaf dan ganin Yadda ake tuwon dawa, mai saukin hadidiya.
Abubuwan hadawa
- Nikeken garin dawa
 - Kanwa
 - Ruwa
 
Yadda ake hadawa
- Da farko zaki dora tukunyarki a wuta ki sa ruwa daidai misali
 - Idan ya tafasa sai ki debo garin dawarki da ki ka tankade kisa ruwa ki dama ki zuba a kan tafasasshen ruwan.
 - Sai ki sa mucciya ki juya don kar ya yi gudaje. Sai ki kawo ruwan kanwa kadan ki zuba ki barshi yayi ta dahuwa.
 - Idan yayi sai ki tuka zaki ga har yauki yake yi. Idan kin gama tukawa sai ki rufe ya dan turara, zaki ji yana kamshi sai ki malmala. Za a iya ci da miyar kubewa ko miyar kuka.
 
Photo credit: Haleema Waxeerie

