A yau za mu gabatar muku da Miyar ayoyo da kubewa a nan shafin mu na Bakandamiya Kitchen.
Abubuwan hadawa
- Ayoyo
- Kubewa
- Attarugu
- Albasa
- Manja
- Maggi
- Gishiri
- Kayan kamshi
- Nama
- Daddawa
Yadda ake hadawa
- Da farko zaki wanke namanki kisa albasa da maggi ki dora a wuta ki tafasa.
- Sai ki wanke kubewarki ki goga da abin goga kubewa ki ajiye a gefe.
- Bayan nan sai ki wanke ayoyonki ki yanka ki ajiye a gefe.
- Sai kuma ki duba namanki idan yayi sai ki sauke ki juye a wani abu.
- Sannan sai ki maida tukunyar wuta ki sa manja da albasa ya dan soyu, sai ki zuba namanki ki soya shi sama sama.
- Sai ki jajjaga attarugu da albasa ki zuba ki daka daddawa da kayan kamshi, sai ki zuba ki sa ruwan tafasashen nama ki dan kara ruwa sai ki zuba maggi da gishiri sai ki rufe ya tafasa.
- Idan yayi sai ki zuba kubewarki ki barshi kamar minti 4-5 sai ki zuba ayoyonki ki sa kanwa ka dan sai ki barshi kamar minti 5, sai ki juya sosai zaki ga yayi yauki, sai ki sauke ki taba kiji..
Zaki iya ci da kowane irin tuwo. Na gode.
Photo Credit: Worldlytreat.com